Kwankwasiyya
Yar siyasa a jihar Kano, Hajiya Naja’atu Mohammed ta soki Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya butulcewa Rabiu Musa Kwankwaso bayan sun shafe shekaru tare.
An shiga jimami bayan rasuwar Alhaji Muhammad Nasir Isah Tsauri, shugaban tafiyar Kwankwasiyya a Katsina; Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yaba da jajircewarsa.
Dr. Yusuf Bello Danbatta ya kare Gwamna Abba Yusuf, inda ya ce bai ci amanar Kwankwaso ba. Ya ce sauya sheka al'ada ce a siyasar Kano da Kwankwaso ya fara.
A labarin nan, za a ji cewa har yanzu ana matsa lamba domin a hade tsofaffin yan takarar Shugabannin kasa, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso a zaben 2027.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya karbi 'yan Kwankwasiyya mazauna Dubai a tafiye-tafiye da ya yi zuwa kasar waje. Ya yi magana kan sauya shekar Abba Kabir.
Dr. Yusuf Bello Danbatta ya yi sharhi kan sauya shekarar Gwamna Abba Yusuf zuwa APC. Ya ce "ba a sarki biyu a gari ɗaya" don haka Abba ya bar Kwankwasiyya.
Kungiyar mabiyar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da aka fi sani da Kwankwasiyya ta jinjinawa mataimakin gwamnan Kano, Aminu Gwarzo da sauran yan amana.
Majalisar dokokin Kano ta bayyana cewa labarin da ake yadawa cewa ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan Kano, Aminu Gwarzo daga mukaminsa ba gaskiya ba ne.
An samu rashin fahimtar juna a taron jam'iyyar APC a jihar Kano. Wannan shi ne taron farko da ya hada 'yan bangaren Abba Kabir Yusuf da Abdullahi Ganduje.
Kwankwasiyya
Samu kari