Zaben jihohi
Gwamnan jihar Kogi, kuma dan takarar shugabancin gwamnan jihar Kogi karkashin jam'iyyar APC, Yahaya Bello, ya bayyana a wanda ya lashe zaben jihar a karamar hukumar Ijumu ta jihar Kogi.
Gwamnan jihar Kogi kuma dan takarar jam’iyyar APC, Yahaya Bello, ya maka abokan adawarsa, Musa Wada na jam’iyyar PDP da Natasha Akpoti ta jam’iyyar SDP a akwatin da ya kada kuri’a. Akwatinsa ne mai lamba 11 da ke gundumar Okene-Eb
An gano tsohon sanata mai wakiltan mazabar Kogi ta Yamma, Dino Melaye a cikin wani hoto da ya yi kama da cewa yana rabawa masu kada kuri'a kudi a mazabarsa. Daily Nigerian ta ruwaito cewa an dauki hoton ne cikin sirri kafin Mista
Gabannin zaben gwamnan jihar Kogi da za a yi a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta saki cikakken jerin dukkanin yan takarar da za su yi takara da jam’iyyunsu.
Wasu da ake zargin yan daban siyasa ne a safiyar Litinin, 11 ya watan Nuwamba, sun kona sakatariyar jam’iyyar Social Development Party (SDP), da ke Lokoja, babbar birnin jihar Kogi.
Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamna na ranar 16 ga watan Nuwamba a jihar Kogi, Musa Wada, ya bayyana cewa zai jagoranci jihar cikin tsoron Allah idan aka zabe shi.
Rade-radin na yawo cewa PDP ta fara shiga rikici kan wanda za ta ba tikiti a 2023. Sai dai jam’iyyar tace ba ta dauki wata matsaya game da tikitin takarar shugaban kasa na 2023 ba tukun.
A yayin da zaben gwamnan jihar Kogi ke kara karato wa, 'yan kabilar Igala a karkashin jagorancin sabon mataimakin gwamna jihar Kogi, Edward Unekwuojo Onojo (CIK), Sanata Jibrin Isa Echocho, da sauran zababbun mambobin jam'iyyar AP