INEC da Jami’an tsaro sun murde zaben da aka yi a Kogi da Bayelsa - Fayose

INEC da Jami’an tsaro sun murde zaben da aka yi a Kogi da Bayelsa - Fayose

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Peter Fayose, ya yi magana a game da zaben gwamnonin jihohin Kogi da Bayelsa da aka gudanar Ranar Asabar dinnan, 16 ga Watan Nuwamban 2019.

Mista Ayodele Fayose ya fito ya na mai cewa hukumar zabe na kasa mai zaman kanta watau INEC ta murde zaben. Tsohon gwamnan bai yarda da ingancin zaben da aka shirya a jihohi biyun ba.

A wani sako da tsohon gwamnan ya fitar ta dandalinsa na sada zumuntan zamani na Tuwita, ya zargi hukumar zabe na INEC da kuma jami’an tsaron Najeriya da tafka magudi a Kogi da Bayelsa.

Ayo Fayose ya rubuta: “Yau wata rana ce ta takaici da bakin ciki a kasarmu da damukaradiyya ganin yadda INEC da jami’an tsaro su ka murde sakamakon zaben jihohin Kogi da kuma Bayelsa”

Babban jagoran na jam'iyyar PDP a Kudu maso Yammacin kasar ya ja kunnen gwamnatin kasar cewa ka da ta dauki shiru-shirun ‘yan Najeriya a matsayin na’am da mugun nufin da ta ke yi.

KU KARANTA: Ana so hukumar INEC ta soke zabukan Kogi saboda an yi magudi

Mista Fayose ya kara da cewa: "Ka da a yi kuskuren daukar shirun mutanen Najeriya a matsayin yin na’am da manakisar da ake kitsawa. ‘Dan adawar ya rufe jawabinsa da cewa: ‘Ina gargadi!”

Kafin nan tsohon gwamnan na jam’iyyar PDP ya yi gargadi cewa gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi zai amsa duk wata tambaya game da mutanen da aka kashe a cikin jiharsa a lokacin zaben.

Akwai zargin cewa Fayose wanda ya mulki jihar Ekiti tsakanin 2014 da 2018 ya yi amfani da murdiya wajen samun nasara a dawowarsa kan mulki sa’ilin da ya doke gwamna mai-ci na APC.

A zaben da aka yi, kungiyoyi da dama sun yi wa hukumar INEC gardama inda su ka ce jami’an tsaro sun bada gudumuwa wajen yin magudi tare da zargin amfani da kudi wajen sayen kuri’a.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng