2019:Jami’in INEC ya ce an ba shi rashawar N50000 a zaben Gwamnan Kogi

2019:Jami’in INEC ya ce an ba shi rashawar N50000 a zaben Gwamnan Kogi

Mun samu labari cewa wani jami’in hukumar INEC mai zaman kanta da ya yi aiki a Kogi ya ce wani ‘dan siyasa ya ba shi kudi domin a murde zaben jihar ta yadda jam'iyyarsa za ta lashe zabe.

Malamin zaben jihar na Kogi da ba a bayyana sunansa ba, ya gabatar da shaida a zahiri gaban Duniya na wasu tulin kudi da aka mika masa a matsayin cin hanci saboda ya sabawa doka.

Wannan Ma’aikacin hukumar zabe ya yi aiki ne a cikin karamar hukumar Igalamela-Odolu a zaben da aka yi Ranar Asabar 16 ga Watan Nuwamban 2019 yayin da ake zaben gwamnan jihar.

Malamin zaben ya zama abin magana a lokacin da ake tattara kuri’un sakamakon zaben gwamnan da aka gudanar. Ana wannan aikin ne a ofishin INEC da ke babban birnin Lokoja.

The Cable ta rahoto cewa wannan mutumi ya zo da kudin da aka ba shi a matsayinsa na jami’in PO mai tattaro kan kuri’a a karamar hukuma. Wannan kudi dunkulen N500 ne har N50, 000.

KU KARANTA: APC ta ba PDP tazarar kuri'u fiye da 200, 000 a zaben Bayelsa

2019:Jami’in INEC ya ce an ba shi rashawar N50000 a zaben Gwamnan Kogi
Ma'aikacin INEC dauke da kudin da aka ba shi. Hoto daga: The Cable
Asali: UGC

Jaridar ta ce ma’aikacin hukumar INEC din bai bayyana sunan ‘dan siyasar da ya ba shi wannan kudi ba. Haka zalika jami’in bai iya fitowa ya fadi jam’iyyar da ta ke so a murde mata zaben ba.

Babban Ma’aikacin zaben na Garin Igalamela-Odolu ya dai ce an ba sa wannan kudi ne domin ya raba da yaransa. A karshe dai ya tattaro kudin gaba daya ya kawo zuwa ofishin hukumar INEC.

Jam’iyyar hamayya ce ta yi nasara a karamar hukumar Igalamela-Odolu inda Wada Musa ya tashi da kuri’u 11, 000. Jam’iyyar APC mai mulki da ‘dan takararta, Yahaya Ballo, sun samu 8, 075.

Kungiyar nan ta CDD ta zargi ‘yan siyasa da yunkurin sayen jami’an INEC a zaben da aka yi a jihar Kogi. Masu lura da harkar zabe kuma sun nemi a soke zaben gaba daya saboda an yi magudi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel