Nasarar APC: Yahaya Bello babban 'dodo' ne - Oshimhole

Nasarar APC: Yahaya Bello babban 'dodo' ne - Oshimhole

Adams Oshiomhole, shugaban jam’iyyar APC ta kasa, ya kwatanta Yahaya Bello, gwamnan jihar Kogi da ‘babban dodo’ fiye da David Lyon, zababben gwamnan jihar Bayelsa.

A yayin tattaunawa da manema labaran gidan gwamnati, bayan ya gabatar da Bello ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, yace cin zabe a karo na biyu na nuna yayi an gani ne.

Ya kara kwatanta Bello da “jinjiri” kamar yadda ya kwatanta gwamna mai jiran gado na jihar Bayelsa.

Mun hadu da shugaban kasar ne don mika masa jinjiri sabuwar haihuwa daga mahaifar APC a ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba,” in ji shi.

Idan zaku tuna, kwanaki kadan da suka gabata, mun zo nan tare da David Lyon amma wannan ‘babban dodo’ ne muke tare. Saboda shi zamu iya kiranshi da ‘yayi an gani’. Yayi takara kuma ya yi nasara bayan mulki a karon farko da ya yi.

DUBA WANNAN: El-Rufa'i zai jagoranci kwamitin sake duba sayar da wutar lantarki da FG ta kafa

A wurinmu, jam’iyyar APC na takama dashi kuma mun gabatar dashi ga shugaban kasa. Shugaban kasan na alfahari dashi, saboda haka ne ya taya shi murna. Ya yi farin cikin ganin shahadar komawarsa karagarsa.

“Ina da tabbacin cewa, Yahaya Bello zai tunkari mulkinshi karo na biyu da basira. Tunda ya gani kuma ya koyi darussa a mulkinsa na farko. Ba zai yi kasa a guiwa ba wajen ganin cigaba da habakar jihar Kogi.”

A bangaren Gwamna Yahaya Bello, wanda ya karba shahadar komawa karagar mulkin jiharsa daga INEC, ya ce zai iya haduwa da abokan hamayyarsa a kotu matukar sun yanke hukuncin kalubalantar nasararsa.

Ya yi kira ga mutanen jihar Kogi da su goyi bayan mulkinsa a karo na biyu, wanda makasudinsa shine “Habaka hadin kai da kaunar juna a tsakanin kabilun jiha”.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel