An fara maganar tikirin 2023 a PDP bayan kotun koli ta yi hukunci a kan karar Atiku Abubakar
Kusan kwanaki biyu bayan kotun koli ta yi fatali da karar da ‘dan takarar PDP, Atiku Abubakar, ya shigar a gabanta, ya na mai daukaka shari’ar kotun zabe, an fara maida hankali a kan 2023.
Kamar yadda mu ka samu labari daga Daily Trust,wasu daga cikin manyan kusoshin jam’iyyar PDP sun fara tunanin yadda za a fito da ‘dan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2023.
Jaridar ta samu labari daga Majiyar ta cewa wasu gwamnonin masu-ci su na kokarin fito da ‘Dan Arewa a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa a 2023. Sai dai a ba a kama sunayen kowa ba.
Amma wasu Jiga-jigan jam’iyyar hamayyar a Kudancin Najeriya su na ganin cewa za a cuce su idan aka tafi a haka don haka su ke kalubalantar wannan shiri da ake yi na ba Arewa takara.
KU KARANTA: Gudun ayi masa irin na ABiola ya sa PDP Atiku ya makale a Dubai
Wani daga cikin kwamitin amintattu na jam’iyyar watau BOT, ya bayyanawa ‘yan jaridar cewa: “Gaskiya ne ba mu gamsu da Atiku ba, amma aka mika masa tikiti, kuma mu ka goyi bayansa.”
“Yanzu da aka yi fatali da kararmu, akwai koke-koken da ake yi a kan yankin ya kamata su fito da ‘dan takarar shugaban kasa a 2023. Ina tunanin dole Jam’iyya ta yi hattara game da wannan…”
“…Saboda wasun mu da yawa su na tunanin sauya-sheka su koma jirgin APC. Ni kai ina cikin masu wannan tunan, don haka ba zan so in cigaba da yin wannan magana ba kuma.” Inji Jigon.
Sai dai babban Sakataren yada labarai na PDP na kasa, Kola Ologbondiyan, ya sanar da Manema labarai cewa jam’iyyar ba ta dauki wata matsaya game da tikitin takarar shugaban kasa a 2023 ba.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng