Tirkashi: An kama Dino Melaye yana siyan kuri'u (Hoto)

Tirkashi: An kama Dino Melaye yana siyan kuri'u (Hoto)

An gano tsohon sanata mai wakiltan mazabar Kogi ta Yamma, Dino Melaye a cikin wani hoto da ya yi kama da cewa yana rabawa masu kada kuri'a kudi a mazabarsa.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa an dauki hoton ne cikin sirri kafin Mista Melaye ya kada kuri'arsa misalin karfe 9.15 na safe a rumfar zabe ta Iluafor mai lamba 004, Ayetoro 1 a ranar Asabar.

Akwai rahotanni da dama dake nuna cewa 'yan siyasa na siyan kuri'un masu zabe.

Jam'iyyar PDP ta zargi jam'iyyar APC ta shirin sayan kuri'u bayan da gwamnatin tarayya ta bawa gwamnatin Kogi naira biliyan 10 kwanaki uku kafin zabe.

Cibiyar cigaban demokradiya, CDD a ranar Juma'a ta ce akwai alamun cewa an ware kudade masu yawa da za ayi amfani da su wurin sayan kuri'a.

Tirkashi: An kama Dino Melaye yana siyan kuri'u (Hoto)
Dino Melaye yana rabawa masu zabe kudi
Source: Twitter

Baya ga nazarin na CDD, a baya EAC ta ce ana ta raba wa masu zabe kayayyki kamar atamfa da shinkafa a Lokoja da karamar hukumar Karfe na jihar ta Kogi.

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: 'Yan daba sun sace akwatunan zabe a rumfar zaben Dino Melaye

A cikin sanarwar da direktan CDD, Idayat Hassan ta fitar, kungiyar ta ce jami'anta dake bibbiyar harkokin zabe sun gano cewa 'akwai alamun cewa an ware kudade masu yawa domin sayan kuri'u a zaben na ranar Asabar'.

Bugu da kari, bayannan CDD na baya-bayan nan ya nuna cewa ana yunkurin bawa jami'an INEC da sauran ma'aikatan zabe na wucin gadi cin hanci a kananan hukumomi 21 na jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel