Zaben Kogi: Gwamna Yahaya Bello da mataimakinsa sun kawo akwatunansu

Zaben Kogi: Gwamna Yahaya Bello da mataimakinsa sun kawo akwatunansu

- Gwamnan jihar Kogi kuma dan takarar jam'iyyar APC a zaben yau da ke gudana a jihar, Yahaya Bello ya kawo akwatinsa cikin nasara

- Hakazalika, Edward Onoja, mataimakinsa ya kawo akwatinsa mai lamba 1 a gundumar Ogugu da ke karamar hukumar Olamaboro a jihar Lokoja

- A akwatin gwamnan, jam'iyyar APC ta samu kuri'u 716 inda akwatin Onoja ta samu kuri'u 934

Gwamnan jihar Kogi kuma dan takarar jam’iyyar APC, Yahaya Bello, ya maka abokan adawarsa, Musa Wada na jam’iyyar PDP da Natasha Akpoti ta jam’iyyar SDP a akwatin da ya kada kuri’a.

Akwatinsa ne mai lamba 11 da ke gundumar Okene-Eba/Agassa/Ahache, karamar hukumar Okene ta jihar Kogi.

Gwamnan ya samu kuri’u 716 inda ya make Akpoti da Wada wadanda basu samu ko kuri’a daya ba.

DUBA WANNAN: Ma'aikatan INEC sun tsere daga wurin zabe bayan sun sha bugu a hannun 'yan daba

Jaridar Premium Times ta ruwaito yadda gwamnan ya wuce Akpoti da tazara kadan a akwatinta da kuri’u biyu. Ta kalubalanci salon zaben yankinta na mazabar Kogi ta tsakiya.

Edward Onoja, mataimakin Yahaya Bello wanda yayi zabe a akwati na 1 na Emoyokwu da ke gundumar Ogugu, karamar hukumar Olamaboro da ke jihar, ya kawo akwatinsa cikin nasara.

A akwatin da Onoja ya saka kuri’a, APC ta samu kuri’u 934 inda PDP ta tashi a tutar babu.

A cikin wannan nasarar ne jam’iyyar ANRP ta samu kuri'a daya sai lalatatun kuri’u shida a akwatin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel