Zaben Kogi: 'Yan daba sun kona shugaban mata na PDP a gidanta

Zaben Kogi: 'Yan daba sun kona shugaban mata na PDP a gidanta

Wasu da ake zargin 'yan bangar siyasa ne sun kone wata mata a gidanta da ke Ochadamu, karamar hukumar Ofu da ke jihar Kogi kurmus. Abun ya faru ne bayan zaben da aka yi na kujerar gwamnan jihar da aka yi a ranar Asabar da ta gabata.

Matar mai suna Acheju Abuh itace shugaban mata ta jam'iyyar PDP a gundumar Wada/Aro na yankin. An kurmusheta ne kuwa a ranar Litinin da rana bayan da 'yan dabar suka zarge ta da biyayya ga jam'iyya mai mulki.

A gano cewa, 'yan daban sun kusta cikin gidan matar ne da wajen karfe 2 na rana inda suka rufe duk wata hanya da zata iya fita. Sun watsa fetur a gidan tare da kunna wuta.

DUBA WANNAN: Yadda 'yan sanda suka kashe mutum 2 yayin tukin ganganci

'Yan dabar da ake zargin sun hana mutanen yankin kaiwa matar taimako sakamakon harbin da suka dinga wanda ya tsorata mutane duk suka tsere. Hankulan 'yan daban bai kwanta ba har sai da suka ga gidan ya kone kurmus.

Matar ta yi yunkurin gudu ta taga amma ta kasa saboda karafuna da ke tagar tare da harbin da suka dinga aunawa ta inda take.

Mai magana da yawun 'hukumar 'yan sandan jihar Kogi, William Aya, ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya ce, sun samu rahoto ne daga wani mutum mai suna Musa Etu a karamar hukumar Ofu din da wajen karfe 4:30 na yamma a ranar 18 ga watan Nuwambar.

A kone gidan da suka yi, gobarar sai da ta shafi wasu gidaje uku da ke da makwaftaka da gidan matar. A halin yanzu, gawarta na ma'adanar gawarwaki ta asibitin koyarwa na Anyigba don bincike.

"A halin yanzu, jami'an 'yan sanda tare da jami'ai na musamman suna wajen da abun ya faru don hana cigaban tashin-tashinar. Ana cigaba da bincike", Aya yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel