Yadda a ka bi dare da duhu a ka kwacemin nasarata - Dino Melaye

Yadda a ka bi dare da duhu a ka kwacemin nasarata - Dino Melaye

Dino Melaye, dan takarar kujerar sanatan yankin Kogi ta yamma karkashin jam'iyyar PDP, ya ce bai aminta da sakamakon zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta fitar ba.

Hukumar zaben mai zaman kanta ta sake zaben yankin ne kamar yadda kotu ta bada umarni. A sakamakon zaben da suka bayyana, Smart Adeyemi na jam'iyyar APC ne ke jagora. Akwai tazarar kuri'u masu tarin yawa tsakaninsa da Dino Melaye na jam'iyyar APC. Lamarin da yasa Melaye ya ce bai aminta da sakamakon ba.

Dino ne ya yi nasara ne zaben farko da aka yi, a don haka ne ya bayyana sakamakon zaben a karo na biyu da "Almara".

A zantawar da Melaye ya yi da manema labarai a Abuja, ya zargi Adeyemi da Gwamna Yahaya Bello da amfani da tashin-tashina, barazana da tada hankulan mutane a yankunan da suka san ana son shi.

DUBA WANNAN: Magudin zabe: An bukaci INEC ta soke zaben jihar Kogi gaba daya

Ya ce, "Mutane uku a ka harba kuma biyu sun mutu; mutane hudu ne suka mutu a Lokoja; mutane bakwai sun rasa rayukansu a yankin gabas na jihar nan. Rahotannin da a ka samu kenan banda wadanda suka samu raunika daga harbin bindiga."

Melaye ya kara da zargin cewa, sakamakon zaben Iyara, kauyensu Adeyemi duk na bogi ne. An firgita tare da hargitsa kauyen Aiyetoro-Gbede wanda hakan ya jawo mutuwar dan dan'uwansa, Olajuwon.

Ya ce, "Muna jira mu ga abinda hukumar zabe mai zaman kanta zata yi. Amma dukkan sakamakon da aka bayyana ban amince da su ba kuma kirkirarru ne. Ni, Dino Melaye na yi nasarar lashe zabe da rana amma APC ta bi dare ta kwacemin nasarata."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel