Yanzu Yanzu: Hankula sun tashi a Kogi yayinda yan iska suka kona sakatariyar jam’iyyar SDP yan kwanaki kafin zabe
- Wasu yan iska sun kai farmaki sakatariyar wata jam'iyya da ke Lokoja, babbar birnin jihar Kogi gabannin zaben gwamna
- Wannan shine karo na biyu da ake kai farmaki sakatariyar jam'iyyar Social Development Party (SDP) cikin sa'o'i 24
- Da farko dai jam'iyyar ta yi zargin cewa akwai wani shiri da ake na kaiwa ayarin yar takarar gwamnan SDP, Barista Natasha Akpoti hari
Wasu da ake zargin yan daban siyasa ne a safiyar Litinin, 11 ya watan Nuwamba, sun kona sakatariyar jam’iyyar Social Development Party (SDP), da ke Lokoja, babbar birnin jihar Kogi.
Sakatariyar ta SDP na fuskantar sakatariyar karamar hukumar Lokoja, a kewayen Paparanda Square.
Da fari an kaima sakatariyar ta SDP hari a ranar Lahadi, bayan wasu mutane da ba a sani ba sun fasa tagogi da kofofinta, inda suka lalata sauran kayayyakin kamfen din da ke sakatariyar.
Da farko dai jam’iyyar ta yi zargin cewa akwai wani shiri da ake na kaiwa ayarin yar takarar gwamnan SDP, Barista Natasha Akpoti hari gabannin zaben ranar Asabar, 16 ya watan Nuwamba.
KU KARANTA KUMA: Wata kungiya ta yiwa Falana wankin babban bargo kan zargin da ya yiwa Buhari
A wani labarin kuma Legit.ng ta rahoto a baya cewa Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ya bayyana cewa yana nan akan jajircewarsa na ganin nasarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben gwamnan Kogi.
Ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 10 ga watan Nuwamba yayinda yake karyata rahoton cewa yana sukar jam’iyyar mai mulki.
A wani jawabi daga Muyiwa Adekeye, kakakinsa, El-Rufai, wanda ya kasance shugaban kungiyar kamfen din APC a zaben, ya ce yana aiki ba dare ba rana domin tabbatar da nasarar Yahaya Bello a karo na biyu.
Adekeye ya kara da cewa kowa ya san cewa El-Rufai na bayar da gudunmawarsa a duk ayyukan da aka basa, sannan kuma cewa “babu abunda zai sha banban a zaben Kogi.”
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng