Zaben gwamnan Kogi: Wada ya yi alkawarin shugabanci da tsoron Allah

Zaben gwamnan Kogi: Wada ya yi alkawarin shugabanci da tsoron Allah

- Musa Wada, dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamna na ranar 16 ga watan Nuwamba a jihar Kogi, ya bayyana cewa zai jagoranci jihar cikin tsoron Allah idan aka zabe shi

- Wada ya bayyana cewa adalci da daidaito zai kasance abunda zai kafa manufarsa a kai ba wai addini da kabilanci ba

- Ya bayyana cewa Allah ya albarkaci jihar da ma’adinai, da kuma kasar nomad a mutane masu himma, inda ya kara da cewa za a yi amfani da hakan wajen kawo cigaba ga mutanen jihar

Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamna na ranar 16 ga watan Nuwamba a jihar Kogi, Musa Wada, ya bayyana cewa zai jagoranci jihar cikin tsoron Allah idan aka zabe shi.

Wada wanda ya bayyana hakan a lokacin gangamin kamfen a Kabba, Kogi ta yamma, ya bayyana cewa adalci da daidaito zai kasance abunda zai kafa manufarsa a kai ba wai addini da kabilanci ba.

Ya bayyana cewa za a nuna daidaito da adalci ga duk wani yanki na jihar wajen rabon mukamai da tallafi.

Ya roki mutanen jihar da kada su yanke kauna kan halin tabarbarewar lamura da jihar ke ciki a yanzu, cewa farin ciki da annashuwa na nan dawowa a karkashin gwamnatinsa.

Ya bayyana cewa za a fara biyan albashi da fansho kan lokaci a karkashin gwamnatin PDP daga watan Janairun 2020.

KU KARANTA KUMA: Rufe iyakokin Najeriya: Buhari ya yanke shawara mai kyau – Jigon PDP

Ya bayyana cewa Allah ya albarkaci jihar da ma’adinai, da kuma kasar nomad a mutane masu himma, inda ya kara da cewa za a yi amfani da hakan wajen kawo cigaba ga mutanen jihar.

A kan haka, Wada ya bayyana cewa zai shirya tattaunawa da masu zuba jari na gida da waje, kan yadda za a yi amfani da wasu ma’adinai wajen samar da ayyuka da arziki ga mutanen jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel