Wannan ba zabe bane; Dino Melaye ya fadi abinda ya faru a Kogi
Tun kafin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sanar da sakamako na karshe a zaben kujerar Sanatan jihar Kogi ta yamma, dan takarar jam'iyyar PDP, Sanata Dino Melaye, ya ce ba zasu amince da sakamakon zaben ba.
A wani faifan bidiyo da ya fitar, Melaye, ya bayyana cewar ba zabe aka yi a jihar Kogi ba.
"An yi amfani da sojoji, jiragen yaki da jami'an tsaro na gaske da na bogi domin firgita masu zabe. Amma duk da haka INEC ta cigaba da gudanar da zabe.
" An yi amfani da jami'an tsaro da bamu san na gaske ne ko na bogi ba wajen sace akwatunan zabe da kuma tafka magudin zaben.
"Muna da shaidu, mun saka hotuna a dandalin sada zumunta don kowa ya ga abinda ya faru, mune muka ci zabe amma sun murde mana. Ba zamu yarda ba, zamu bi hakkin mu," a cewar Dino Melaye.
Kalli faifan bidiyonsa a nan:
Tun kafin bullar faifan bidiyon Dino Melaye, Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa tun kafin a kammala sanar da sakamakon zaben dukkan kananan hukumomin da ke jihar Kogi a zaben da aka yi ranar Asabar, dan takarar jam'iyyar PDP, Musa Wada ya ce bai aminta da sakamakon ba.
A yayin zantawa da manema labarai a garin Lokoja a ranar Lahadi, wanda a lokacin ne ake sanar da sakamakon zaben na kananan hukumomi 21 na jihar, Wada ya zargi cewa sakamakon duk na bogi ne.
Ya ce, abinda ya faru a jihar a cikin ranakun karshen makon ya yi karantsaye ga damokaradiyya da kuma burin mutanen jihar Kogi.
Ya ce, abinda ya faru yayin zaben bai bayyana gaskiyar ra'ayin mutanen jihar ba.
Ya kara da jajanta yadda jami'an tsaro suka hada kai da hukumar zabe mai zaman kanta don dakile ra'ayin mutanen jihar Kogi da suka bayyana ta hanyar kuri'un da suka kada.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng