Kogi 2019: Gwamnati ta bawa babban sarki kyautar irin motar Sarki Sanusi (Hotuna)

Kogi 2019: Gwamnati ta bawa babban sarki kyautar irin motar Sarki Sanusi (Hotuna)

- A yayin da zaben gwamna a jihohin Bayelsa da Kogo ke kara matso wa, manyan masu ci a gwamnatin APC 'yan kabilar Igala sun bawa sarkinsu kyautar babbar motar alfarma

- Sabon mataimakin gwamnan jihar Kogi, Edward Onoja, shine wanda ya jagooranci bikin bayar da kyautar motar ga babban basaraken

- Manyan 'ya'yan na jam'iyyar APC sun ce suna daf da kammala gina wa basaraken wasu manyan gidajen huta wa na alfarma a wasu garuruwan da ke karkashin masarautar

A yayin da zaben gwamnan jihar Kogi ke kara karato wa, 'yan kabilar Igala a karkashin jagorancin sabon mataimakin gwamna jihar Kogi, Edward Unekwuojo Onojo (CIK), Sanata Jibrin Isa Echocho, da sauran zababbun mambobin jam'iyyar APC sun bawa babban saraken kabilar Igala, mai martaba, Attah Igala, kyautar dankareriyar motar alfarma irin ta sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Da yake jawabi yayin bikin gabatar da motar ga basaraken, mataimakin gwamnan ya ce sun bawa sarkin kyautar ne saboda girman kasa da yawan jama'a da yake mulka.

"Akwai bukatar sarkin kabila ta 9 a yawan jama'a a Najeriya ya kasance mai aji, ta yadda duk inda ya shiga za a san cewa babban sarki ne ya zo," a cewar sa.

A nasa bangaren, Sanata Echocho, ya jinjinawa sabon mataimakin gwamnan jihar bisa jajircewa da kuma kishin kabilarsa da ya nuna tare da bayyana cewa suna daf da kammala gina wa sarkin wasu manyan gidajen hutawa na alfarma guda biyu a Dekina da Ankpa.

Kogi 2019: Gwamnati ta bawa babban sarki kyautar irin motar Sarki Sanusi (Hotuna)
Mataimakin gwamna ke yin rawa yayin bayan mika kyautar mota ga Attah Igala
Asali: Twitter

Kogi 2019: Gwamnati ta bawa babban sarki kyautar irin motar Sarki Sanusi (Hotuna)
Gwamnati ta bawa babban sarkin Igala kyautar motar alfarma
Asali: Twitter

Kogi 2019: Gwamnati ta bawa babban sarki kyautar irin motar Sarki Sanusi (Hotuna)
Kogi 2019: Gwamnati ta bawa babban sarki kyautar irin motar Sarki Sanusi
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng