Yahaya Bello ya lashe zabe a karamar hukumar Dino Melaye

Yahaya Bello ya lashe zabe a karamar hukumar Dino Melaye

- Gwamnan jihar Kogi kuma dan takarar shugabancin jihar karkashin jam'iyyar APC, Yahaya Bello, ya kawo karamar hukumar Ijumu

- Karamar hukumar Ijumu ce asalin Dino Melaye da Smart Adeyemi, 'yan takarar sanatan kujerar Kogi ta yamma

- Gwamna Yahaya Bello na jam'iyyar APC ya samu kuri;u 11,425 inda Wada Musa ya samu kuri'u 7,587

Gwamnan jihar Kogi, kuma dan takarar gwamnan jihar Kogi karkashin jam'iyyar APC, Yahaya Bello, ya bayyana a wanda ya lashe zaben jihar a karamar hukumar Ijumu ta jihar Kogi.

Bello ya samu jimillar kuri'u 11,425 a karamar hukumar, inda Wada Musa na jam'iyyar PDP ya tashi da kuri'u 7,587, kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta sanar.

Natasha Akpoti ta jam'iyyar SDP, ta samu kuri'u 223.

A karamar hukumar ta Ijumu, an yi wa masu kada kuri'a 59,578 rijista amma an tantance mutane 20,139. Mutane 19,881 ne suka kada kuri'a. Kuri'u marasa matsala an samu 19,435 inda wadanda ke da matsala suka kai 446.

DUBA WANNAN: Dino Melaye ya sha mugun kaye a karamar hukumarsa

Ga kuri'un da kowacce jam'iyya ta samu:

APC-11,425

PDP-7,587

SDP-223

Karamar hukumar Ijumu a jihar Kogi ce asalin karamar hukumar 'yan takarar kujerar sanatan jihar Kogi ta yamma; Dino Melaye da Smart Adeyemi.

A jihar Kogi, 'yan takara 24 ne suka kara da gwamnan da ke mulki yanzu, Yahaya Bello na jam'iyyar APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng