Labaran garkuwa da mutane
'Yan bindiga da suka sake alƙali Janet Gimba ta kotun gargajiya a Kaduna sun sake ta. Sun buƙaci kudin fansa N150 miliyan nan da kwana 6 ko su cutar da 'ya'yanta.
Gwamnan jihar Benuwai, Rabaran Hyacinth Alia ya sanar da sa dokar zaman gida a ƙaramar hukumar Ukum da kewaye biyo bayan ɓarkewar zanga-zanga a yankin.
Babbar kotun jihar Osun ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga masu garkuwa da mutane da suka kashe wani Bafulatani bayan sun yi garkuwa da shi.
Yan bindiga sun kai farmaki yankin ƙaramar hukumar Giwa a jihar Kaduna, sun yi awon gaba da dagacin Tunburku, Malam Ashiru da wasu manoma a karshen mako.
Amina Adamu, daya daga cikin matan auren da aka sace su a hanyar Takum-Katsina-Ala a jihar Taraba makonni hudu da suka gabata, ta tsero daga hannun masu garkuwa.
Rundunar ƴan sanda reshen jihar Katsina ta bayyana cewa jami'anta sun samu nasarar kama mutum buyu da ake zargi da hannu a sace mahaifiyar Dauda Rarara.
Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindiga kusan 100 sun shiga kauyen Dambaza a ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara, sun yi garkuwa da mutane akalla 47.
'Yan bindiga sun kai farmaki garin Kahutu da ke ƙaramar hukumar Ɗanja a jihar Katsina, sun yi awon gaba da mahaifiyar fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara.
Yan bindigan da suka yi garkuwa da limamin coci, Mikah Suleiman sun ɗauki bidiyonsa yana neman agajin mutane, ya ce rayuwarsa na cikin haɗari a wurin ƴan fashi.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari