Labaran garkuwa da mutane
Yayin da ake jimamin abinda ya faru a Gusau da Dutsin-Ma, yan bindiga sun ƙara sace ɗaibai 4 daga jami'ar jihar Nasarawa da ke Keffi ranar Litinin da daddare.
Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta bayyana cewa dakarunta sun yi nasarar kuɓutar da mutane 171 da aka yi garkuwa da su a faɗin jihar cikin watanni huɗu.
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yankewa wasu mutum biyu da suka yi garkuwa da babban lauyan Najeriya, Mike Ozekhome, hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari.
Wata mahaifiya ta yi ta maza inda ta cafke wani ɗan ta'adda da ya save ɗiyarta sannan ya halaka ta bayan an ba shi kuɗin fansa masu yawa a Zariya.
Wasu tsagerun 'yan bindiga sun yi awon gaba da Manjo Janar mai ritaya, Duru bayan sun masa kwantan ɓauna a jihar Imo da ke Kudu maso gabashin Najeriya.
Masu garkuwa da mutane da suka sace kwamishinan yaɗa labarai na jihar Benuwai sun nemi iyalinsa sun harhaɗa masa Naira miliyan N60m a matsayin fansa.
Tsagerun 'yan bindiga sun sake kai farmaki ƙauyuka biyu a ƙaramar hukumar Munya da ke jihar Neja, inda suka yi awon gaba da mutane sama da 30 harda mata.
An kama wani kasurgumin mai garkuwa da mutane a wani yankin jihar Yobe da ke Arewa maso Gabas. An bayyana yadda aka yi ya shiga hannun jami'an 'yan sanda.
Rundunar Operation Hadarin Daji ta ƙara kubutar da wasu mutane 15 bayan artabu da 'yan bindiga a jihar Zamfara, sun sheke wasu da ciki da yawa yau Litinin.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari