Jihar Kebbi
Gwamma Nasir Idris Kauran Gwandu ya yi ikirarin cewa ƴan bindiga ba su da sansani ko guda ɗaya a jihar Kebbi, daga wasu jihohin makota suke shigowa.
Wasu sarakunan gargajiya a iyakokin Sokoto da Kebbi da ke makwabtaka da Nijar sun musanta zargin cewa an ba sojojin Faransa mafaka domin kassara kasar.
Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum.ya halarci taron kaddamar da littafin da aka rubuta domin karrama Gwamnan Kebbi, Nasir Idris Kauran Gwandu.
Gwamnatin jihar Kebbi karkashin jagorancin Gwamna Nasir Idris ta yi rabon babura ga ma'aikatan gidan gwamnati. Ta ce ta yi hakan ne domin hana fashi.
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi alhini kan rasuwar Mai Shari’a Uthman Argungu inda ya yaba gudunmawarsa ga kasa, tare da yin addu’ar Allah ya jikansa.
Sarkin Gwandu da ke jihar Kebbi, Mai Martaba Muhammad Ilyasu Bashar ya yabawa salon mulkin Shugaba Bola Tinubu inda ya ba shi shawara kan jan al'umma a jiki.
Wata mai yi wa kasa hidima (NYSC), ta riga mu gidan gaskiya a jihar Kebbi. Matashiyar ta rasu ne bayan ta fadi, inda aka yi kokarin farfado da ita amma ba a dace ba.
Dakarun sojojin Najeriya sun ci gaba da bude wuta kan 'yan ta'addan Lakurawa. Sojojin sun lalata sansanonin 'yan ta'addan da ke a jihohin Kebbi da Sokoto.
Gwamnatin Bola Tinubu ta shirya tsaf wurin tabbatar da samun ingantaccen tsaro a Arewacin Najeriya bayan ta tura dakaru na musamman domin yakar yan Lakurawa.
Jihar Kebbi
Samu kari