Katsina
Dan majalisar dokokin jihar Katsina mai wakiltar Matazu, Hon. Ibrahim Dikko Umar, ya bayyana cewa mutanen mazabarsa na cikin tashin hankali saboda 'yan bindiga.
Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da kai hari masallacin kauyen Unguwan Mantau da ke yankin karamar hukumar Malumfashi a Katsina, an kashe mutane 13.
Sojin saman Najeriya sun kai farmaki a sansanin 'yan bindiga da ke Danmusa, jihar Katsina, sun kubutar da mutum 62, gwamna Radda ya yaba da jarumtar jami’an tsaro.
Wasu manoma a jihar Katsina sun koma gonaki cikin kwanciyar hankali, inda wasu suka ce shekaru da dama basu yi noma ba amma yanzu rayuwa ta sauya.
Gwamnatin Katsina ta ce kashi 87% na kananan hukumomi sun samu tsaro, sai Faskari, Kankara da Matazu da ke cikin matsananciyar barazanar ’yan bindiga.
Bayan wata daya da rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a birnin London da ke Birtaniya, ma’aikatan gidansa a garin Daura sun yi jimamin rasuwarsa.
Gwamna Dikko Umaru Radda na Katsina ya shirya fita ketare domin yin hutu har na tsawon mako uku saboda kula da lafiyarsa ana tsaka da jita-jitar lafiyar Bola Tinubu.
A labarin nan, za a ji cewa wani Mai Unguwa a Katsina, Salisu Abdullahi ya shaida wa jami'an tsaro yadda ya ke jan 'yan ta'adda don kai hari kauyuka.
Majiyoyi sun ce karamar hukumar Safana a jihar Katsina ta kulla yarjejeniyar sulhu da ‘yan bindiga, kamar Jibia, Batsari, da Danmusa, domin zaman lafiya.
Katsina
Samu kari