Kasashen Duniya
China ta kara haraji kan kayayyakin Amurka zuwa 125% yayin da rikicin kasuwanci ya kara kamari. China ta ce ta shirya yin karar Amurka gaban hukumar WTO.
Rahotanni sun tabbatar da cewa hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta kammala aikin tantance sunayen mutum 109 da za su zama jakadun Najeriya a kasashen ketare.
Gwamnatin sojan Nijar ta ayyana Hausa a matsayin harshen kasa, mataki da ke kawar da Faransanci da kuma nuna kishin yare da ikon ‘yan kasa. Amma an ce wasu na adawa.
Saudiyya ta karyata rahoton da ke cewa an hana kasashe 13 neman biza. Ta ce babu sabon takunkumi, sai dai ka’idar Hajji ga masu bizar yawon shakatawa.
Gwamnatin tarayya ta fara tantance wasu 'yan siyasa da ake shirin nada wa a matsayin jakadun Najerya bayan shafe watanni babu wakilci a kasashen waje.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya tashi daga Abuja zuwa birnin Dakar da ke kasar Senegal domin wakiltar Bola Tinubu a wani babban taro.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya shirya tafiya zuwa birnin Paris na kasar Faransa domin yin hutun kwanaki 14. 'Yan Najeriya sun yi masa martani mai zafi.
Kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso sun kakaba harajin kashi 0.5% kan kayayyakin da ke shigowa daga mambobin kasashen ECOWAS ciki har da Najeriya.
Masana falaki sun tabbatar cewa jinjirin watan Shawwal zai kasance a sararin samaniya, amma saboda matsalolin yanayi da warwatsewar haske, ba zai yiwu a gan shi ba.
Kasashen Duniya
Samu kari