Kasashen Duniya
Kasar Iran ta yi magana kan ɓarnar da hare-haren Isra'ila suka yi mata inda ta ce yaki da Isra’ila ya jawo mummunar barna a cibiyoyin nukiliya na kasar.
Jagoran addinin Musulunci ta Iran, Ayatullah Ali Khamenei ya yi magana bayan shafe kwana fiye da 10 ana yaƙi da Isra'ila inda ya bugi kirji kan nasararsu.
Wasu daga cikin mazauna birnin Beersheba sun ce harin da Iran ta kai masi kafin dojar tsagaita wuta ta fara aiki ya gigita su, wasu sun ce sun ɗauka ƙarshensu ya zo.
Kasar Isra'ila ta bayyana hasarar da Iran ta jawo mata a yakin da suka yi da Iran. An kashe mutanen Isra'ila 28 tare da jikkata 3,000 da lalata motoci 4,000.
Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce su kansu kasashen Iran da Isra'ila sun galabaita, don haka ya jaddada cewa batun yaƙi ya kare, za a koma teburin tattaunawa.
Duk da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da aka yi tsakanin Iran da Isra'ila a jiya Talata, jagoran addini a kasar, Ayatullah Ali Khamenei bai ce komai ba.
Bayan sulhu da tsagaita wuta a tsakani, Isra'ila ta kinkimo wani babban zargi kan Iran game da daukar nauyin ta'addanci wanda ta daura laifn kan babban bankin kasar.
Wasu sojojin Isra'ila bakwai sun mutu a Gaza bayan harin bam da ya tarwatsar motar da suke ciki. Hamas ta ɗauki alhakin kai wannan mummunan harin.
A labarin nan, za a ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce akwai damuwa a tattare da mutumin da Bola Tinubu ya ce abokin Karatunsa ne.
Kasashen Duniya
Samu kari