Jihar Kaduna
Shugabanni a Arewacin Najeriya da suka hada gwamnoni da sarakunan gargajiya sun nuna damuwa kan sabon kudiri da ke gaban Majalisar Tarayya na haraji.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar ya bukaci shugabannin yankin Arewacin Najeriya da su magance matsalar almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta.
Gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya sun gana babban hafsan sojohi (CDS), Janar Christopher Musa da sauran masu ruwa da tsaki kan matsalolin yankin.
Kamfanin TCN ya bayyana cewa ya hada kai da ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro domin gyara layin wutar lantarkin Arewa da ta lalace.
Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana cewa ya rage adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar. Uba Sani ya sanar da hakan ne bayan ya gana da Shugaba Bola Tinubu.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya yi magana kan tsuke bakin aljihun gwamnati. Gwamnan ya ce tun bayan hawansa mulki rabin albashi yake karba.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a jihar Kaduna. Miyaguk 'yan bindigan sun yi awon gaba da wasu manoma har guda hudu tare da sace kayan abinci.
Sheikh Abubakar Salihu Zariya ya ziyarci Sheikh Usman Riji Riji Attalili Attaguzuty. An ba babban malamin Izala Darika yayin ziyarar. Mutane sun tayar da kura.
Allah ya yiwa ɗan marigayi sarkin Zazzau rasuwa, Alhaji Ibrahim Shehu Idris ya rasu bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a asibitin koyarwa na ABU a Shika.
Jihar Kaduna
Samu kari