Jihar Kaduna
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya jajantawa iyalan Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi wanda ya rasu a ranar 3 ga watan Afrilun 2025 da muke ciki.
Atiku Abubakar, Nasir El-Rufa'i, Aminu Waziri Tambuwal, Isa Ali Pantami, Abubakar Malami SAN sun ziyarci shugaba Muhammadu Buhari a jihar Kaduna.
Kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki a Abuja, Eko, Enugu, Ikeja, Jos, Kaduna, Kano da Yola sun tsunduma a cikin matsala saboda aringizon kudin wuta.
An samu barkewar mummunan fada a tsakanin wasu 'yan bindiga masu gaba da junansu a jihar Kaduna. Rikicin ya yi sanadiyyar kashe miyagun 'ƴan bindiga guda 10.
Wani magidanci, Abubakar Aminu ya kashe dan uwansa Sani Yusuf a Zariya, yayin da a Agwara, wasu mutum shida suka kashe wani Alhassan bisa zargin satar waya.
Tsohon shugaban kasa a Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce ya bar mulki da dukiyar da ya mallaka tun kafin ya zama shugaban kasa ba tare da ta ƙaru ba.
A Kaduna, 'yan bindiga sun sace Fasto Samson Ndah Ali daga gidansa a Mararaba Abro. Sojoji da 'yan sanda sun bi sahun wadanda suka yi garkuwa da shi.
Gwamnonin jam'iyyar APC mulki a Najeriya sun ziyarci tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a Kaduna. Sun bukaci ya tsoma baki kan ficewar na kusa da shi.
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya tuna da ma'aikatan da suka yi ritaya da wadanda suka rasu. Gwamnan ya umarci a fitar da kudade domin biyansu hakkokinsu.
Jihar Kaduna
Samu kari