Jihar Kano
Gwamnatin Kano ta bullo da shirin yi wa 'yan daba afuwa. Ta bayyana cewa mutanen da za su amfana za a sake dawo da su cikin al'umma bayan an gyara musu tarbiyya.
Bayan shafe kusan wata guda a birnin London na Birtaniya, tsohon shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya dawo Najeriya bayan rade-radin jinya.
Mahaddacin Kur'ani a daga Najeriya a jihar Kano ya zamo na uku a gasar Kur'ani da aka yi a kasar Saudiyya. Buhari Sanusi Idris ya samu kyautar Naira miliyan 163.
A labarin nan, za a ji yadda gwamnan Kano, Injiniya ya rantsar sababbin jami'an gwamnatinsa, daga ciki har da Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci', Sa'idu Yahaya.
A labarin nan, za a ji cewa wata baiwar Allah mai suna Maryam Hussaini Abdullahi ta gamu da iftila'in alakanta jakarta da tulin wiwi a kasar Saudiyya.
Rundunar yan sandan Kano ta gurfanar da wadanda ake zargi da tayar da zaune taaye a zaben cike gurbim da aka gudanar a mazabun yan majalisa 2 ranar Asabar.
A labarin nan, za a ji cewa jigo a jam'iyyar adawa ta NNPP, Injiniya Buba Galadima ya yi kaca-kaca da ƴan siyasa da ke neman madafun iko don mulkar talaka.
Bayan ta da jijiyoyin wuya kan ganin yan sanda a Kano suna taimakawa dan siyasa rabon kuɗi ga jama'a, rundunar ta tabbatar da ɗaukar matakin ladabtarwa kan jami’an.
Shahararren jarumin fina-finan Kannywood, Mato Yakubu wanda aka fi sani da Malam Nata’ala ya yi bayani kan mawuyacin hali na jinya da yake ciki inda ya roki al'umma.
Jihar Kano
Samu kari