Jihar Kano
A labarin nan, za a ji cewa gwamnatin jihar Kano ta bayyana daukar nauyin dalibai sama da 200 da za su yi karatu a jami'o'i daban daban a Najeriya.
Tsohon shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci addu'o'i da karatun Kur'ani a Kano. Maguzawa 280 sun karbi addinin Musulunci a gidansa da ke Kano.
A labarin nan, za a ji cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta bayyana cewa a shirye ta ke wajen raba matasan Kano da dabi'ar fadan daba da kwacen wayoyin jama'a.
A labarin nan, za a ji yadda dalibai da ke zaman gidan fursun saboda laifuffuka daban-daban suna daga cikin mutanen da su ka yi nasara a jarrabawar NECO ta bana.
Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da sababbin sauye-sauyen gwamnati da suka shafi kwamishinoni biyu da manyan sakatarori a jihar.
Ana hasashen cewa jihohin Arewa, kamar Kebbi, Taraba, da Adamawa za su samu ruwan sama da iska mai karfi. NiMet ta yi gargadi kan yiwuwar ambaliya.
Gwamnatin jihar Kano ta bukaci mutane su kiyaye matakan lafiya domin gujewa kamuwa da zazzabi mai tsanani da ke sa zubar da jini, ta fitar da matakai uku.
Tsagin jam'iyyar NNPP ya bayyana cewa ba ya tare da Rabiu Musa Kwankwaso kan maganar shiga jam'iyyar APC. NNPP ta ce ta riga ta kori Kwankwaso da Kwankwasiyya.
A labarin nan, za a ji cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta sanya rana biyan wasu daga cikin 'yan fanshon jihar Kano bashin N5bn na gwamnatin Ganduje.
Jihar Kano
Samu kari