Jihar Kano
Jam’iyyar NNPP mai adawa a Najeriya ta ce za ta tsallake rikicin siyasa a Kano duk da jita-jitar cewa Gwamna Abba Yusuf na shirin sauya sheka zuwa APC.
Kungiyar masu ba da shawara na musamman ga gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, sun yi matsaya kan siyasar jihar. Sun jaddada biyayyarsu ga Gwamna.
Jagoran siyasar Kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce zai sauya sheƙa zuwa wata jam’iyya ne kawai idan aka ba shi tikitin shugaban ƙasa ko mataimaki a 2027.
Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya nuna damuwa kan rikicin siyasar Kano, yana kira ga ’yan siyasa da su dakatar da duk wani abu da ke kara rarrabuwar kai.
Gwamnatin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ta nesanta kanta daga batur tarbar mai martaba Aminu Ado Bayero a filin jirgin Malam Aminu Kano daga tafiya.
Jagoran NNPP na kasa, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa babban bacin ransa shi ne daukar gwamnatin da suka sha wahala a mika wa Ganduje.
Madugun Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan batun sauya sheka. Ya ce zai ci gaba da zama a jam'iyyar NNPP.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa Rabiu Kwankwaso da ya shirya kwace mulkin jihar Kano daga hannun Abba bayan gwamnan ya iara kokarin tsayawa da kafarsa.
Majiyoyi sun ce manyan jiga-jigan jam'iyyar NNPP a Najeriya a kananan hukumomi 44 na Kano na matsa wa Gwamna Abba Yusuf ya koma APC mai mulkin kasar.
Jihar Kano
Samu kari