Jihar Kano
Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa yana cikin tattaunawa da abokansa na siyasa kan makomarsu gabanin babban zaben 2027.
Tsohon sanata mai wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawa, Sanata Kabiru Gaya, ya fice daga jam'iyyar APC. Sanata Kabiru Gaya ya koma jam'iyyar ADC.
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya nemi a dawo da shi gidan yarin Kurmawawa da ke Kano daga Kuje da ake rufe da shi a Abuja. Ya mika bukata ga kotu.
A labarin nan, za a ji cewa Garba Kore Dawakin Kudu ya shawarci Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya tabbata ya naɗa mataimakin da zai taimaka masa wajen cin zabe a Kano.
Shugaban masu rinjaye na Majalisar dokokin Kano, Lawan Hussaini ya bayyana cewa babu bukatar ci gaba da shirin tsige Aminu Abdussalam Gwarzo tun da ya ajiye aiki.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau na shirin komawa APC bayan ganawa da Bola Tinubu gabanin zaben shekarar 2027.
A labarin nan, za a ji cewa kamfanin da ke aiki a makarantar FGCK ya yi bayanin rawar da gwamnatin Kano ta taka wajen ba shi kwangila makarantar.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya nada Kwamishinan muhalli a matsayin mukaddashin kwamkshinan ma'aikatar albarkatun ruwa na jihar bayan Umar Doguwa ya yi murabus.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sanar da cewa yana nan daram a ADC duk da matsalolin da suke fuskanta. Ya amsa tambaya kan nenan shugaban kasa a zaben 2027.
Jihar Kano
Samu kari