Jihar Kano
Wasu mata da ke yin gurasa a Kano, sun yi zanga-zanga don nuna rashin jin dadinsu kan karin kudin fulawa, sun ce karin kudin ya jefa sana'arsu cikin wani hali.
Shugaban jam'iyyar APC, Dakta Abdullahi Ganduje ya roki addu'a ga tawagar Super Eagles don samun nasara a wasanta da kasar Angola a gobe Juma'a a gasar AFCON.
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya shaida cewa an hana su mu’amala da kudinsu da ke banki. Dabarar shi ne za a janye kudi a duk lokacin da suka shigo.
Jigon jam'iyyar NNPP, Jamu Mohammed ya musanta maganar sasanta tsakanin Rabiu Kwankwaso da Umar Ganduje inda ya ce bai su san da wannan magana ba.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya yi magana kan gayyatar da Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa Gwamna Abba ta shiga jam'iyyar APC.
Wani mai gadi a kwalejin Prestige International, Nurudeen Shehu, mai shekaru 37, ya dauki rayuwarsa da kansa saboda tsohuwar matarsa ta kara wani aure a Kano.
Sanata Kawu Sumaila ya ki amincewa da bukatar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na maye gurbin Babban daraktan dake kula da bangaren gas, Mansur Kuliya da Oluwole.
An samu rahotanni biyu na wani mai gadin makaranta da almajiri da suka sheke kansu a jihar Kano. Shi mai gadin ya dauki ransa ne saboda tsohuwar matarsa ta yi aure.
Alƙalin da ke shari'ar Ɗanbilki Kwamanda ba shi da lafiya saboda haka ba zai iya sauraren shari'ar a yau ba, an ɗage shari'ar zuwa Maris mai zuwa.
Jihar Kano
Samu kari