Jihar Kano
Kamar yadda Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya yi zaman fada tare da hakimai a yau Lahadi an ce shi ma Aminu Bayero, tsohon Sarkin Kano, ya yi zaman fada a Nassarawa.
Gwamnatin tarayya ta hannun ma'aikatar gina gidaje da raya birane ta sanya tushen ginin sababbin gidaje a jihar Kano da nufin magance karancin wurin zama.
Dambarwar Kanona ci gaba da daukar dumi, inda gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ce babu yadda zai yi mata dole kan soke masarautun Kano biyar da nada sabon sarki.
Shaharraren malamin addinin Musulunci a jihar Kano, Sheikh Lawal Triumph ya yi kira kan daukar mataki a yadda aka wayi gari da sarakuna biyu a Kano.
Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan sarautar Kano, tsohon hadimin shugaban majalisar dokokin jihar, Hassan Cikinza Rano ya bayyana cewa an tafka kura-kurai.
Gwamnatin jihar Kano ta mika kokon bararta ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Gwamnatin ta bukaci Tinubu ya shiga tsakani a rikicin masarautar Kano.
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya samu goyon bayan hakimai 40 cikin 65 na jihar. Hakan na nufin cewa mafi rinjayen hakiman Kano sun yi mubayi'a ga sabon sarki.
Gwamnatin jihar Kano ta hannun mataimakin gwamna, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ta nemi afuwar Nuhu Ribadu kan zarginsa da hannu a rikicin masarautar Kano.
Rundunar sojojin Najeriya ta musanta cewa jami'anta na da hannu a rikicin masarautar Kano. Rundunar ta ce an tura sojojin ne domin hana karya doka da oda.
Jihar Kano
Samu kari