Jihar Kano
A ranar farko na zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin tarayya ne wasu bata-gari su ka rika fasa shaguna tare da dibar kayan mutane da sunan sun ci ganima.
Bashir Alhassan mai shekara sama da 60 ya na cikin wadanda suka fita zanga-zanga a Kano. Tsohon ya shaidawa Legit abin da ya fitar da shi kan tituna a shekarunsa.
Mai martaba sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga matasa da su yi taka tsantsan, kar su bari ayi amfani da su wajen rusa Kano da Arewa.
Rundunar 'yan sandan Katsina ta bayyana matsayarta na tabbatar da kakkabe 'yan daba daga cikin masu gudanar da zanga-zanga a jihar, inda aka kama yan daba 50.
Duk da yadda aka samu tashe-tashen hankula a wasu jihohin kasar nan saboda zanga-zanga, jama'a sun fara taruwa a Legas domin fara tattakin matsin rayuwa.
Gwamnatin Kano ta ce ta sassauta dokar hana fita ta awanni 24 da ta sanya a fadin jihar a jiya Alhamis domin ba al'umma damar zuwa masallacin Juma'a.
Kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, Olumuyiwa Adejobi ya fitar da hotuna da kuma bidiyo na yadda masu zanga-zanga ke satar dukiyar jama'a a Kano a ranar Alhamis.
Rundunar Kano sun bayyana nasarar cafke karin matasan da ake zargi da fasa wuraren ajiyar kayan abincin jama'a tare da wasosonsu a ranar Alhamis.
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnoni hudu sun sanya dokar hana fita ta awanni 24 a jihohinsu yayin da zanga zangar lumana ta rikide zuwa tashin hankali.
Jihar Kano
Samu kari