Jihar Kano
Sarkin Kano, mai martaba Muhammadu Sunusi II ya kammala karatunsa a fannin shari'ar addinin musulunci da ya fara bayan tsige shi a 2020 a birnin Landan.
An tabbatar da mutuwar mutum huɗu tare da ɓatan wasu mutane shida bayan wnai jirgin ruwa ya kife a kauyen Kauran Mata da ke ƙaramar hukumar Madobi a Kano.
Gwamnatin Kano ta bayyana matsayarta kan zargin da ake yi na cewa an ba kamfanin kanin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso kwangilar magani ba bisa ka'ida ba.
Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta Kano (PCACC), ta samu umarni domin rufe wani asusu da ke dauke da kudade a binciken da take kan badakalar kwangila.
Shugaban ƙungiyar shuwagabannin NNPP na jihohi, Tosin Odeyemi, ya ce ya zama tilas ƴan Najeriya sun shure batun addini ko ƙabila a lokacin babban zaɓen 2027.
Rahotanni sun bayyana cewa kimanin mutane 43 ne suka mutu a wasu jihohin Najeriya sakamakon cin abinci mai guba. Wannan lamari ya fara firgita jama'a.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC), ta kare matakinta na sanya kudaden siyan fom da tsada domin yin takara a zaben kananan hukumomin jihar.
Hukumar PCACC ta kama wasu mutane biyar da suka hada da dan uwan Kwankwaso, Musa Garba, Alhaji Mohammed Kabawa, babban sakataren ma’aikatar kananan hukumomi.
Jam'iyya mai mulki a Kano, NNPC ta sayawa kwamitin tantance yan takarar katin duba jarrabawar kammala sakandare ta WAEC da NECO da kuma yi masu gwajin kwaya.
Jihar Kano
Samu kari