Jihar Kano
Ana zargin wani matukin tirela da wurgo wani dan Karota da ya shiga motar shi domi duba takardun kayan da ya dauko. Lamarin ya faru wajen gadar Muhammadu Buhari.
A cikin watan Afrilu kadai, an yi yunƙurin kutse gidan Kashim Shettima, an yi zargin hana shi shiga Villa, sannan an yi zargin rikici ya balle a kan idonsa.
Bayan gwamnan Delta ya shiga APC, shugaban jam'iyyar na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya ce wasu gwamnoni daga PDP za su sauya sheƙa zuwa cikinta kafin zaɓen 2027.
Jam'iyyar NNPP reshen jihar Kano, ta nuna rashin damuwarta kan sauya shekar da Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, ya yi zuwa APC mai adawa a jihar.
Tsohon kakakin majalisar Kano, Kabiru Alhassan Rurum, wanda yanzu ke wakiltar Rano, Kibiya da Bunkure a majalisar wakilai, ya sanar da ficewarsa daga NNPP zuwa APC.
Babbar kotu a Kano ta yanke wa matashi Sagiru Rijiyar-Zaki hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe mahaifiyarsa da 'yar uwarsa shekaru biyu da suka wuce.
Sanata AbdulRahman Kawu Sumaila ya bayyana dalilin ficewarsa daga jam’iyyar NNPP da cewa ya samo asali ne daga bukatar kare al’ummarsa da cika alkawuran da ya ɗauka.
Hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya ce za su yi maraba da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso da gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC.
Sanata Kawu Sumaila ya tabbatar da cewa ya ajiye NNPP, yayin da ya ƙi bayyana jam'iyyar da ya koma,duk da ana hasashen zai iya faɗawa jam'iyya mai mulki ta APC.
Jihar Kano
Samu kari