Jihar Kano
Gwamnatin jihar Kano, ta koka kam matsalar karancin ruwa da ake.fama da ita a.jihar. Ta zargi gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje da lalata tashoshin samar da ruwa.
Abdullahi Ganduje ya ce APC za ta karɓi Rabi'u Musa Kwankwaso idan ya dawo, yana mai cewa za su taimaka masa domin kar siyasarsa ta mutu murus a inda yake.
Shugaban APC a Kano, Abdullahi Abbas, ya zargi gwamnatin jihar da yaudarar jama'a, ya ce dole APC ta dawo mulki a zabe mai zuwa ta kowane irin hali.
Sanata Barau Jibrin ya goyi bayan kudirin da Sanata Kawu Sumaila ya gabatar kan kisan Hausawa 'yan Farauta a Edo. Barau ya ce za su tabbatar an hukuntasu.
Rikicin cikin gida a NNPP ya kara ta’azzara a Kano, inda manyan jiga-jigan jam'iyyar suka rabu da Kwankwaso, ciki har da Alhassan Rurum da Madakin Gini.
Ɗan Sarki Muhammadu Sanusi II wanda kuma shi ne Tafidan Kano, Adam Lamido Sanusi ya kai ziyara ta musamman ga shugaban APC a jihar, Hon. Abdullahi Abbas.
Wata amarya, Saudat ta kashe angonta Salisu a Kano ta hanyar daba masa wuka a wuya bayan aurensu na kwanaki 9. An ce ma'auratan sun yi auren soyayya ne.
Khalifa Muhammadu Sanusi II ya isa kasar Tunusia domin hhalartar babban taron tattali na FITA2025. TYa samu rakiyar Sarkin Shanun Kano da Jarman Kano.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nada Malam Haladu Mohammed Mai Ba da Shawara kan Inganta Ilimi. Wannan nadin na daga cikin matakan gwamnati inganta ilimi.
Jihar Kano
Samu kari