Jihar Jigawa
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya yi alhinin rashin da aka yi a jihar Jigawa, ya roki Allah ya gafartawa waɗaɓda suka rasu a gobarar da ta afku a Majia.
Karamin ministan man fetur ya bukaci a fara bincike kan dalilin hadarin tankar man fetur a Jigawa. Hadarin ya jawo mutuwar mutane sama da 100, da dama sun jikkata.
Gwamnatin tarayya ta shiga alhinin asarar rayuka bayan fashewar tankar fetur da ta salwantar da rayuka akalla 107 a Jigawa bayan takar fetur ta kama wuta.
Uwargidan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Remi Tinubu ta mika sakon ta'aziyya kan mutanen da suka rasu sakamakon fashewar tankar man fetur Jigawa.
An samu asarar rayuka bayan wata tankar mai ta gamu da hatsari a jihar Jigawa. Mutane kusan 100 ne suka rasu yayin da wasu mutum 50 suka samu raunuka.
A wannan labarin, za ku ji cewa rundunar yan sandan reshen Jigawa ta samu nasarar cafke wasu daga cikin mugayen yan fashi da makami da su ka addabi yankin.
A ranar Asabar 5 Oktoba, 2024 ne aka yi zaben Ciyamomi wasu jihohi hudu, inda daga cikinsu aka, zaben jihohi biyu sun yi matukar daukar hankalin jama'a.
Rundunar 'yan sandan jihar Jigawa ta samu nasarar cafke wani matashi bisa zarginsa da cinnawa kakarsa wuta. Bincike ya nuna matashin na da tabin hankali.
Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya dakatar da hadiminsa bayan ya yi ikirarin cewa ya amince zai biya ma'aikata sabon mafi karancin albashi na N70,000.
Jihar Jigawa
Samu kari