Isra'ila
Ana cigaba da rikici tsakanin Iran da Isra'ila, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya bayyana cewa ba makamin nukiliya ne ke damun kasashen yamma.
Bayan harin Amurka kan kasar Iran, manyan 'yan majalisa daga jam'iyyar Democrat sun caccaki Donald Trump bisa kai hari ba tare da sanar da su ba.
Bayan harin Amurka a Iran, ministan harkokin wajen kasar ya gargadi Amurka kan hare-haren da ta kai, yana cewa “za su fuskanci illa mai dorewa” daga kasar.
Rundunar sojin Isra'ia ta tabbatar da cewa Iran ta sakw harbo makamai masu linzami zuwa ƙasarta, an tabbatar da cewa mutane 11 na kwance suna karɓar magani.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da Amurka ta kai kan Iran, tana cewa hakan barazana ga zaman lafiya a duniya baki ɗaya da yankin Gabas ta Tsakiya.
Donald Trump ya ce Amurka ta kammala kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliya guda uku a Iran. Wannan mataki ya nuna goyon bayan Amurka kai tsaye ga Isra'ila.
Dakarun rundunar sojin Isra'ila sun yi ikirarin kakkaɓo jirage marasa matuƙa da ke ɗauke da bam waɗanda Iran ta yi nufin farmar kasar jiya da daddare.
Yayin da ake ci gaba da yaki da Isra'ila, jagoran addini a Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya zaɓi malamai uku da za su gaje shi idan aka kashe shi.
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya bayyana cewa shugaban Iran ya kira shi a waya, kuma sun tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi shirin nukiliya.
Isra'ila
Samu kari