Isra'ila
Adadin wadanda suka jikkata a Isra’ila ya haura 6,131 yayin da rikicin yaki ke ci gaba tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran tun daga karshen watan Fabrairun 2026.
Makamai masu linzami daga Iran sun afka wa tsakiyar Isra'ila a ranar Laraba, inda suka jikkata mutane tara tare da janyo gobara a yankunan Bnei Brak da Petah Tikva.
Ministan tsaron Amurka Pete Hegseth ya ce suna sane da yadda China da Russia ke taimakawa Iran a yakin da ake ciki, kuma suna daukar matakan dakile wannan goyon baya
Shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar da cewa Amurka za ta janye daga yaki da Iran ko ba a cimma yarjejeniya ba. Ya bayyana haka ne a fadar White House.
Rundunar IRGC ta Iran ta jero kamfanonin Amurka irin su Tesla da Google a matsayin halattattun wuraren kai hari idan aka ci gaba da kashe mata shugabanni.
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi magana kan tattaunawa inda ya ce kasar ba ta neman tsagaita wuta, sai dai cikakken tsarin kawo karshen yaki.
Ministan tsaron kasar Isra'ila, Israel Katz ya ce kasar na shirin mamaye wasu yankunan kudancin Lebanon ko bayan yaki da Hezbollah yayin da ake yaki da Iran.
Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC), ta kaddamar da hare-hare kan Amurka da Isra'ila a yankin Gabas ta Tsakiya yayin da ake yaki.
Fadar White House ta bayyana cewa shugaban Amurka zai so kasashe Larabawa su biya shi makudan kudin da ya kashe a yaki da kasar Iran da ya kai hare-hare.
Isra'ila
Samu kari