Gwamnan Jihar Katsina
Abun bakin ciki ya faru a ranar Juma’a 16 ga watan Fabrairu a jihar Katsina lokacin da mai ba Gwamna Aminu Masari shawarar na musamman akan al’amuran addini, Abdullahi Darma, ya take yarsa, A isha da mota bisa tsautsayi.
Gidauniyar Ukashatu wanda ta shirya tallafi na musamman ga mata 300 masu kananan sana’o’i irin su kosai, awara, da kuli-kuli. Gidauniyar ta kuma samawa ‘yan makaranta kayan karatu da su ka hada da litattafai da tebura da sauran su
Mun samu labari cewa Mai Girma Gwamna Masari zai kashe kudi wajen aikin titi a Katsina. Gwamnatin Jihar Katsina za tayi sababbin hanyoyi sannan kuma Gwamnatin Jihar za kuma ta gina wasu gidaje a fadin Jihar duk a bana.
Jami'ar tarayya da ke Dutsinma a jihar Katsina ta bayyana cewa ta dawo da wasu ma’aikata 250 da shugabancin da ta gabata ta kora daga aiki ba bisa ka'ida ba. Shugaban Jami'ar ya ce tuni an biya ma’aikatan kudin alawus na su.
Gwamna Masari ya amince zai cika gurubin wasu sakatarori na dindindin da kuma nada wasu sabo su hudu a jihar. Har zuwa yanzu sanarwa daga gwamnati ba ta bayyana ranar da za a rantsar da sabbin sakatarorin ba ..
Gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar shirin Fadama III na gwamnatin jihar Katsina, ta ce za ta tallafawa kimanin manoman tumatir 100 da kayan aikin gona a cikin yankuna 10 a Daura don bunkasa nomar tumatir a jihar.
Gwamnatin jihar Katsina ta ce za ta dauka malaman makarantu fiye da 5,000 a makarantun firamare na jihar don bunkasa ma'aikatan ilimi. Gwamna Masari ya ce za a fara daukar malaman makarantun a cikin farkon kwata na 2018.
Ance yana da farfyadiya, amma 'yan-sanda na tantama ko duka ne yayi ajalinsa. Su dai iyayen yarinya sunce ya fadi ne ya yanke da kyaure, bayan da aka gaya wa saurayin cewa bazai auri yarinyar ba, inda kuma wai shima yace tana da..
Jam'iyyar APC reshen jihar Katsina ta yi watsi da yiwuwar gudanar da zaben kananan hukumomi don sanya wakilai a jihar. Shugaban jam'iyyar ya ce wannan mataki ya kasance mai yiwuwa har lokacin da kotu ta yanke hukunci a kan batun.
Gwamnan Jihar Katsina
Samu kari