Sheikh Pantami ya bude wani muhimmin aiki da hukumar sa ta yiwa Katsinawa
Hukumar inganta fasahar zamani ta kasa (NITDA) da Sheikh Isa Ali Pantami, ke jagoranta ta bude wata cibiyar raya fasahar zamani a jihar Katsina.
A wata takardar sanarwa da jami’ar hulda da jama’a ta hukumar NITDA, Hadiza Umar, ta fitar ta sanar da cewar cibiyar ta Katsina na daya daga cikin irin cibiyoyin 6 da hukumar zata bude a yankuna 6 na Najeriya.
Kazalika ta bayyana cewar bude cibiyar na daga cikin kokarin gwamnatin shugaba Buhari na kawo karshen matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa.
Cibiyar da aka bude na cikin wata makaranta da gwamnatin jihar Katsina ta gina domin bawa matasan jihar yin karatun difloma da na digiri a bangaren fasahar sarrafa bayanai ta zamani.
A jawabinsa, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, wanda sakataren gwamnatin jihar, Mustapha Inuwa, ya wakilta, ya bayyana cewar tuni gwamnatin jihar ta fahimci muhimmanci ilimin fasahar zamani a bangaren magance rashin aiki ga matasa.
DUBA WANNAN: Zazzabin wata zai haifar da matsanancin duhu a Najeriya ranar Juma'a
A jawabin shugaban NITDA, Sheikh Pantami, ya nuna jin dadinsa bisa gudunmawa da hadin kan da gwamnatin jihar Katsina ke basu domin hada gwuiwa wajen kawo cigaba ga matasa ta hanyar basu horo a fasahar sarrafa bayanai ta zamani
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng