Jam'iyyar PDP ta koka da irin makukun bashin da Buhari ya jawowa Najeriya

Jam'iyyar PDP ta koka da irin makukun bashin da Buhari ya jawowa Najeriya

Mun ji cewa babbar Jam’iyyar adawa a Najeriya PDP ta koka da irin makudan bashin da Gwamnatin APC ta Shugaba Buhari ta karbowa Najeriya daga hawan ta mulki a 2015 zuwa yanzu. Don haka PDP tace APC ta shirya faduwa zabe a 2019.

Jam'iyyar PDP ta koka da irin makukun bashin da Buhari ya jawowa Najeriya
Gwamnatin Buhari ta ci bashin Tiriliyan 9 a shekaru 3

A halin yanzu, bashin da ke kan Najeriya ya haura Naira Tiriliyan 20 wanda Gwamnatin Shugaba Buhari kadai ta ci kusan rabin wannan kudi. PDP tace da ace Buhari ya bar wadanda su ka san harkar tattalin arziki sun yi aiki da duk ba haka ba.

KU KARANTA: Manyan ‘Yan takara 10 da za su nemi doke Buhari a Jam'iyyar PDP

Sakataren yada labarai na PDP Kola Ologbondiyan ya bayyana cewa a cikin shekaru 3 da Jam’iyyar APC tayi a kan mulki, babu wani tsarin tattalin arziki na kirki da Shugaban kasa Buhari ya kawo sai dai karbowa Najeriya tarin bashi kurum.

PDP tace ana tafka satar hauka a Gwamnatin nan ta APC. PDP ta zargi NNPC da yin gaba da wasu kudi fiye da Naira Tiriliyan 10 na kwangilar shigo da man fetur da aka ba manyan ‘Yan APC. Ana kuma zargin an sace rarar kudin mai da ake samu.

Jam’iyyar adawar tace da Gwamnatin Tarayya tana adana abin da ake samu, da ba a kai ga cin wadannan makudan bashi ba. PDP ta kuma koka da yadda jama’a su ka rasa aikin yi da kuma irin yunwa da talaucin da aka jefa mutane a ciki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng