Bikin Babbar Sallah: Buhari ya isa Daura

Bikin Babbar Sallah: Buhari ya isa Daura

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya isa mahaifar sa, garin Daura, dake jihar Katsina bayan ya bar Abuja da yammacin yau, Litinin.

A dazun ne Legit.ng ta sanar da ku cewar rahotannin da ta samu sun tabbatar mata da cewar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bar Abuja domin tafiya zuwa mahaifarsa, Daura, dake jihar Katsina inda zai yi bukukuwan sallah babba.

A dazu ne Legit.ng ta sanar da ku cewar a yau Litinin ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, yayi ganawar sirri tare da shugabannin hukumomin tsaro a fadar sa dake Abuja, kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto.

Bikin Babbar Sallah: Buhari ya bar Abuja zuwa Daura
Buhari yayin barin Abuja domin tafiya Daura

Bikin Babbar Sallah: Buhari ya isa Daura
Buhari ya isa Daura

A rahotanni da aka tattara, an gano cewa wannan ya kasance daya daga cikin ayyuka masu muhimmanci da shugaban kasar ya fara gudanarwa bayan dawowar shi Abuja daga hutun kwana 10 da yayi a birnin Landon.

DUBA WANNAN: Almundahana da babakere: An tsige shugaban karamar hukuma a jihar Kebbi

Anyi ganawar ne a ofishin shugaban kasa da misalin karfe 11:27 na safe.

Sai dai ba a gabatar da bayanai akan dalilin da yasa aka yi ganawar sirrin mai muhimmanci ba.

A ranar Asabar da ta gabata ne shugaba Buhari ya dawo daga birnin Landan na kasar Ingila inda ya shafe tsawon kwanaki 14 a wani takaitaccen hutu da ya yi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel