Mutuwar Ibrahim Coomassie: Mun shiga cikin dimuwa matuka – Kungiyar Dattawan Arewa

Mutuwar Ibrahim Coomassie: Mun shiga cikin dimuwa matuka – Kungiyar Dattawan Arewa

Kungiyar tuntuba ta Arewa, ACF ta bayyana kaduwarta matuka da samun labarin mutuwar shugabanta, Alhaji Ibrahim Coommassie, Sardaunan Katsina, tsohon babban sufeta janar na Yansandan Najeriya, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Coommassie ya rasu ne a ranar Alhamis, 19 ga watan Yuli a garin Katsina yana mai shekarau Saba’in da shidda, kamar yadda Kaakakin ACF, Muhammad Ibrahim Biu ya bayyana.

KU KARANTA: Allah ya yiwa tsohon sifeto Janar na yan sandan Najeriya, Ibrahim Coomassie rasuwa

Mutuwar Ibrahim Coomassie: Mun shiga cikin dimuwa matuka – Kungiyar Dattawan Arewa
Ibrahim Coomassie

Kaakakin yace: “Coommassie mutum ne mai tsananin kishin yankin Arewa, tare da son cigabanta da kuma raya ayyukan Ahmadu Bello Sardauna, haka zalika mutum ne cikakke, jajirtacce wanda yayi fice a duk aikin da yayi.”

ACF tace ba wai Arewa ba kadai, hatta Najeriya kwata ta yi babban rashi da mutuwar Coommassie, mutum da yayi riko da adalci, yanci, da’a da kuma rashin nuna wariya ko son kai.

Daga karshe ACF ta aika da ta’azziyarta ga masarautar Katsina, gwamnatin jihar Katsina, gwamnatin Najeriya, jama’an jihar Katsina da ma al’ummar Najeriya gaba daya, tare da fatan Allah ya jikanshi da gafara, Amin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng