'Yan PDP sun kai karar Masari Kotun Koli
- Ana cigaba da kai ruwa rana tsakanin gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina da jam'iyyar PDP a jihar
- Rikcin ya samo asali ne tun lokacin da Masari ya soke shugabanin kananan hukumomi a watan Yulin 2015
- Shugabanin kananan hukumomin sun shigar da gwamnan kara a kotun koli bayan rashin nasara a babban kotun Katsina
Jam'iyyar adawa ta PDP tana kallubalantar soke shugabanin kananan hukumomi da gwamna Aminu Masari ya yi a jihar Katsina.
A yau Talata, PDP ta shigar da kara a kotun koli inda take bukatar kotun ta soke kwamitin rikon kwarya da gwamnan ya kafa a kananan hukumomi 34 da ke jihar a watan Augusta.
Ciyaman din PDP na jihar, Salisu Majigiri ne ya bayar da wannan sanarwan a wata taron manema labarai da ya kira a Katsina.
A cewarsa, jam'iyyar ta shigar da kara a kotun koli saboda rashin amincewa soke shugabanin da kafa kwamitocin riko da gwamna Aminu Bello Masari ya yi.
DUBA WANNAN: Kwankwaso ya gano matsalar da yasa shugabanin baya suka gaza canja Najeriya
"Mun shigar da kara a babban kotun Katsina daga baya kuma muka daukaka kara a kotun daukaka kara da ke Kaduna saboda bamu gamsu da hukuncin da aka zartar da farko ba.
"Yanzu shari'ar tana kotun koli inda muke sauraron hukuncin da za'a zartar amma duk da haka gwamnatin jihar tayi gaban kanta ta kafa haramtattun kwamitin riko." inji Majigiri.
Kazalika, Majigiri ya ce ma'aikatan kananan hukumomi 23 cikin 34 da gwamnan ya rushe sun shigar da kara a babban kotun Katsina inda suma suke kalubalantar matakin da gwamnan ya dauka.
Ya ce shugabanin kananan hukumomin suna bukatar kotu da haramtawa gwamnan kafa kwamitin riko a kananan hukumomin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng