Mutane fiye da 10 sun fara harin kujerar Gwamnan Borno a APC

Mutane fiye da 10 sun fara harin kujerar Gwamnan Borno a APC

Labari ya zo mana daga Yerwa Express cewa akalla mutum 16 ne ke neman gaje kujerar Gwamna Kashim Shettima a Jihar Borno a APC. Yanzu haka dai wa’adin Kashin Shettima yana daf da karewa.

Mutane fiye da 10 sun fara harin kujerar Gwamnan Borno a APC
Ana rububin kujerar Gwamna Kashim Shettima a Jihar Borno.
Asali: Depositphotos

‘Yan takarar Jam’iyyar APC mai mulki da-dama su na neman Gwamna ya sa baki domin a ba su tikitin Jam’iyya. Shi dai Mai Girma Gwamna Kashim Shettima ya tubure ya nuna cewa Ubangiji ne zai zabi Shugaba ba wai Gwamnan Jihar ba.

Sai dai Gwamnan ya soki wasu ‘Yan siyasar Jihar da ke Abuja wadanda ya kira da marasa kishi. Duk da haka Gwamnan bai nuna cewa ga ‘Dan takarar da zai so ya mikawa karagar mulki ba kamar yadda ake yi a wasu Jihohi irin Yobe da sauran su.

KU KARANTA: Ba zan yi takara da Shugaba Buhari ba - Shekarau

Kusan dai fadar Gwamnan Jihar ta rabu kashi 3 a game da zaben Magajin Kashim Shettima. Kawo yanzu dai ga jerin masu neman kujerar Gwamnan na a APC wanda a ciki har da wani Ministan Buhari da kuma Sanatoci da ‘Yan Majalisun Jihar.

1. Umar Alkali Nasko

2. Hon. Abba Jato

3. Sanata Mohammed Abba Aji

4. Hon. Mohammed Makinta

5. Mustapha Baba Shehuri

6. Mutawalli Kashim Ibrahim Imam

7. Ambasada Baba Ahmed Jidda

8. Idris Mamman Durkwa

9. Farfesa Babagana Umara Zulum

10. Barr. Kaka Shehu Lawan

11. Adamu Lawan Zaufanjinba

12. Adamu Yuguda Dibal

13. Sanata Abubakar Kyari

14. Sanata Bakaka Garbai

15. Hon. Babagana Tijjani Banki

16. Alhaji Mai Sheriff

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel