Gwamnatin Tarayya za ta saki Biliyan 12.15 na aikin ruwa a Jihar Katsina
Mun samu labari daga Jaridun kasar nan jiya cewa Majalisar zartarwa na Gwamnatin Tarayya watau FEC ta amince a saki makudan Biliyoyin kudi saboda wani aikin ruwa da za ayi a Jihar Katsina.
Ministan ruwa na Najeriya ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta duba maganar aikin ruwa na Zobe da ke Garin Katsina inda ta amince a fitar da kudi har Naira Biliyan 12.15 domin karasa wannan muhimmin aiki da ya gagara.
Suleiman Adamu wanda shi ne Ministan harkokin ruwa ya bayyanawa manema labarai wannan a jiya bayan taron Ministoci da aka yi a fadar Shugaban kasa. Tun 1992 dai aka soma wannan aiki amma aka gaza karasawa har ila yau.
KU KARANTA: Buhari ya isa Ribas domin kaddamar da wani muhimmin aiki a filin jirgi
Gwamnatin Shugaba Buhari na kokarin cigaba da ayyukan da aka manta da su a Kasar don haka ta tado da wannan kwangila da aka gaji aka bar shi. Ministan na kasar yace zai zama an kashewa aikin ruwan na zobe kudi sama da Naira Biliyan 20.
Ana sa rai za a gama aikin nan da shekara daya da rabi idan aka saki wadannan kudi. Za dai ayi karo-karo ne tsakanin Ma’aikatar ruwa ta Tarayya da kuma Gwamnatin Jihar Katsina domin cin karfin wannan aikin inji Injiniya Sulaiman Adamu.
Dazu kuma kun samu labari cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai bude katafariyar Jami’ar Sojojin da aka gina a cikin Garin Biu da ke Kudancin Jihar Borno a Ranar Talatan nan mai zuwa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng