Abubuwan da Gwamnatin Shugaban kasa Buhari tayi a Jihar Katsina

Abubuwan da Gwamnatin Shugaban kasa Buhari tayi a Jihar Katsina

Wannan karo mun kawo maku wasu ayyukan da Gwamnatin Tarayya tayi ko kuma ta ke daf da shirin farawa ko ya Jihar Katsina inda nan ne Mahaifar Mai Girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kan sa.

Abubuwan da Gwamnatin Shugaban kasa Buhari tayi a Jihar Katsina
Gwamnatin Shugaba Buhari za ta gina titin dogon jirgin kasa zuwa Nijar
Asali: Facebook

Hamza Ukasatu Matazu wani babban Masoyin Gwamna Aminu Bello Masari kuma daya daga cikin manyan magoya bayan Gwamnatin Shugaba Buhari da APC shi ne ya kawo jerin wadannan manyan ayyuka.

Ga dai wasu daga cikin kokarin da Gwamnatin Tarayya tayi a Katsina:

1. Jami’ar Sufuri a Garin Daura

Wannan Gwamnati tana da shirin fara gina Jami’a ta harkar sufuri ta Tarayya a Garin Daura a Jihar Katsina. Wannan Jami’a da za a fara shekara mai zuwa za ta ci akalla Dala Miliyan 50 watau Naira Biliyan 18.

2. Makarantar horas da Jami’an DSS

Haka kuma Gwamnatin Tarayya ta amince a gina wajen koyon aikin tsaro na DSS watau masu fararen kaya a Jihar Katsina. Hukumar DSS din za ta gina wannan wuri ne domin horas da Jami’an ta a Garin Musawa.

KU KARANTA: Mulkin Buhari ya sa wani Matashi ya nemi ya kashe kan sa a Garin Yola

3. Titin dogo har zuwa Kasar Nijar

Gwamnatin Buhari tana da shirin gina titin dogo mai tsawon kilomita fiye da 200 wanda zai ratso tun daga Kasar Kano ta cikin Dambatta zuwa Kazaure, har Garuruwan Daura, Mashi, sannan ya kare a cikin Kasar Nijar.

4. Kamfanin tatar man fetur

Gwamnatin Buhari ta amincewa wani babban ‘Dan kasuwa a Katsina ya gina matatar danyen mai a Garin Mashi da ke Jihar Katsina. Gwamnatin Buhari ta ce wannan aiki zai yi sanadiyyar samawa mutane aikin yi.

5. Makarantar Sakadare ta Sojoji

Ma’aikatar tsaro a karkashin Gwamnatin Tarayya tare da hadin-kan Gwamnatin Jihar Katsina za ta gina Makarantun Sakandare watau ‘Command’ a Garuruwan Faskari da kuma Kurfi a cikin Jihar Shugaban kasa.

Idan ba ku manta ba, jiya kun ji cewa a makon nan ne Gwamnatin Tarayya ta amince a saki makudan Biliyoyin kudi har Naira Biliyan 12.15 saboda wani aikin ruwa da za ayi na Zobe da ke Jihar Katsina.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng