'Yan sanda sun damke wata budurwa da ke yiwa 'yan achaba fashi a Katsina

'Yan sanda sun damke wata budurwa da ke yiwa 'yan achaba fashi a Katsina

Hukumar 'yan sanda reshen jihar Katsina sun gano wata dabara da kungiyar wasu barayin babur ke amfani da ita na amfani da 'yan mata da za su hau acaha sannan su bawa dan achabar alewa mai dauke da kwaya da za ta bugar dashi kafin sauran 'yan fashin su bayyana.

Mun samo daga Daily Trust cewa hukumar 'yan sanda reshen jihar Katsina ta damke wata budurwa, Zinatu Abubakar mai shakaru 19 da tayi yunkurin sace babur din wani matashi bayan ta dirka masa kwayoyi.

Sanarwar da jami'in hulda da jama'a na rundunar, Gambo Isa ya bawa manema labarai a ranar Alhamis na Katsina na cewa. budurwar tana aiki ne tare da wasu gungun barayi da suka dade suna adabar mutanen Katsina.

'Yan sanda sun damke wata budurwa mai yiwa 'yan acaba fashi
'Yan sanda sun damke wata budurwa mai yiwa 'yan acaba fashi
Asali: Facebook

Isa ya ce wanda ake zargin ta bawa mai babur din, Gide Wada kwayar ne a lokacin da ya dauko ta daga Kofar-Kaura zuwa Sokoto Rima Quaters duk a garin Katsina.

DUBA WANNAN: A karo na farko bayan tsige shi, Lawal Daura ya yi magana kan mamaye majalisa

Kakakin 'yan sandan ya ce mai babur din ya tsaya a lokacin da ya fara ganin jiri bayan Zinatu ta bashi Chocolate a hanyarsu ta tafiya inda zai kaita.

Kamar yadda ya ce, bayan mai babur din ya tsaya sai wadanda ke aiki tare da Zinatu, Abubakar da Chairman suka garzayo inda ya ke su kayi kokarin kwace babur din.

Ya yi bayannin cewa barayin zun ruga cikin daji yayin da suka lura hayaniyar da su keyi yana janyo hankalin mutane. Mutanen daga baya sun cafke Zinatu kuma suka mika ta ga jami'an yan sanda.

Isa ya yi ikirarin cewa wanda ake zargi da laifin ta amsa laifinta kuma ta kara da cewa ta dade tana aikata irin wannan laifin a Kaduna da Kano.

Daga karshe ya shawarci masu achaba su guji karban abinci ko abin sha daga mutanen da basu sani ba don gudun fadawa cikin irin wannan tarkon da zai janyo ayi musu fashi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel