Matsin lamba daga EFCC: Tsohon gwamnan PDP Shema ya garzaya kotun daukaka kara

Matsin lamba daga EFCC: Tsohon gwamnan PDP Shema ya garzaya kotun daukaka kara

- Tsohon gwamna jihar Katsina, Ibrahim Shema ya garzaya kotun daukaka kara domin hana kotun tarayya cigaba da shari'ar tuhumarsa da ake na handamar kudi

- Sai dai kotun daukaka karar ba ta amince da bukatar tsohon gwamnan ba dakatar da sharia'r da EFCC ta shigar a kansa

- A yanzu, lauya mai wakiltan Ibrahim Shema ya sake neman kotu ta kara masa lokaci domin ya shirya yada zai kare wanda ya ke wakilta

Tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema ya bukaci kotun daukaka kara da ke zamanta a Kaduna ta soke hukuncin da babban kotun tarayya da ke Katsina da yanke a ranar 23 na watan Afrilun 2018 na bawa EFCC ikon cigaba da tuhumarsa.

Matsin lamba daga EFCC: Tsohon gwamnan PDP Shema ya garzaya kotun daukaka kara
Matsin lamba daga EFCC: Tsohon gwamnan PDP Shema ya garzaya kotun daukaka kara
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Dan Sule Lamido ya lashe takarar kujerar Sanata a PDP

Lauyan Shema, E.C Ukala SAN ya gaza gamsar da Alkali Babagana Ashgar cewar kotun ba ta da ikon sauraran tuhumarsa da akeyi na aikata laifuka 26 da suka shafi karkatar da kudaden gwamnati.

Saboda hakan ne Shema ya garzaya kotun daukaka karar inda ya bukaci ta soke hukuncin da karamar kotun ta yanke.

Lokacin da aka karanto karar a yau 2 ga watan Oktoban 2018, lauyan wanda ake kara P.Y kura SAN ya sanar da alkalan kotun uku cewar yana da wata shari'ar ya kuma roki kotun ta kara masa lokaci domin ya shirya yadda zai kare wanda ya ke wakilta.

Lauyan masu shigar da kara, S.T. Ologunorisa SAN bai yi jayaya ga bukatar P.Y Kura ba. Su ma alkalan kotun, karkashin jagorancin Justice Bidiya Shata sun amince da bawa lauyan Shema karin lokaci domin ya shiryawa.

Kotun da dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 22 ga watan Oktoban 2018.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel