Osinbajo, Ganduje da Masari sun ziyarci yayar Buhari a Daura, hotuna
A yau, Alhamis, ne mataimaki kuma mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, tare da gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, da takwaransa na jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da kuma shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, suka ziyarci, Hajiya Rakiya Adamu, yayar shugaba Buhari.
Tun da rana jaridar Legit.ng ta kawo maku labarin cewar Osinbajo ya isa garin Daura dake jihar Katsina domin yiwa dan takarar sanata a karkashin jam’iyyar APC yakin neman zabe.
Osinbajo ne zai jagoranci tawagar yakin neman zaben sanatan da za a gudanar biyo bayan mutuwar sanatan dake wakiltar yankin, kamar yadda Laolu Akande, mai taimakawa Osinbajo a bangaren yada labarai ya sanar.
Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da takwaransa na jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ne suka tarbi Osinbajo bayan ya sauka a Katsina kafin su dunguma su wuce zuwa garin Daura.
DUBA WANNAN: Majalisa ta gimtse hutun da ta tafi, zasu dawo cikin satin mai zuwa
Bayan isar sa garin Daura, Osinbajo ya wuce kai tsaye ya zuwa fadar sarkin garin, Farouk Umar Farouk, domin yin gaisuwa. "Manufar jam'iyyar APC da gwamnatin shugaba Buhari ita ce inganta rayuwar talakan Najeriya," Osinbajo ya shaidawa sarkin na Daura.
A nasa jawabin, sarkin Daura ya tabbatarwa da Osinbajo cewar mutanensa na tare da shugaba Buhari da kuma gwamnatinsa dari bisa dari.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng