Zaben maye gurbi a Katsina: INEC zata dauki ma'aikata 7,727 a Katsina
A kalla mutane 7,727 hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) zata dauka aiki na wucin gadi a zaben maye gurbi a jihar Katsina.
INEC zata gudanar da zaben maye gurbin sanatan yankin Katsina ta Arewa, Sanata Mustapha Bukar, da Allah ya yiwa rasuwa.
Kwamishinan zaben jihar Katsina, Alhaji Jibril Ibrahim Zarewa, ne ya sanar da hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da INEC gudanar ranar Alhamis, a Katsina.
Zarewa ya bayyana cewar, majalisar dattijai ta sanar da INEC, cikin wata wasika da ta aika wa hukumar ranar 13 ga watan Yuli, cewar akwai bukatar a cike gurbin Marigayi Bukar a majalisar ta dattijai.
Zarewa ya kara da cewa mutanen da za a dauka aikin na wucin gadi sun hada da matasa masu bautar kasa, daliban manyan makarantu da ma'aikatan hukumomin gwamnati dake aiki a jihar.
DUBA WANNAN: 'Yan takarar APC 4 sun hada kai, sun yi korafin fifita Buhari
Zaben zai shafi kananan hukumomi 12 da suka hada da, Baure, Bindawa, Daura, Dutsi, Ingawa, Kankia da Kusada.
Ragowar sune, Mai'adua, Mani, Mashi, Sandamu da Zango.
Kananan hukumomin na da jimillar kuri'u 855,092 a rijistar INEC ta zaben 2015..
Kazalika ya bayyana cewar INEC zata gudanar da sahihin zabe mai tsafta.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng