Wahalar man fetur a Najeriya
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa an sace kimanin ganga miliyan 7.68 na danyen mai a shekarar 2023. Hukumar NEITI ta ba kungiyoyin fararen hula muhimman shawarwari.
Kimanin ’yan kasuwar mai hudu ne suka kashe Naira biliyan 833.49 wajen shigo da mai a cikin watanni tara na farkon shekarar 2024. Sun samu riba mai gwabin gaske.
Ana so Gwamna ya canza sunan sabuwan jamiar da za'a bude ta Khadija University, Majia zuwa sunan ranar da gobarar nan ya faru domin tunawa na har abada.
Kungiyar ƴan kasuwar mai masu zaman kansu IPMAN ta bayyana cewa dillalai na tsallake matatar Ɗangote ne saboda akwai wuraren da suka fi ta arhar man fetur.
Akwai matatu a kasahen duniyan da yanzu babu tamkarsu wajen tace danyen mai. Dangote ya na cikin matatun mai mafi girma da ake ji da su a kasashen duniya.
Jami’an hukumar kwastam ta kasa sun yi nasarar raba Najeriya da fetur da ya kai N71,760,930 idan ya shiga kasuwa, an yi kamen ana shirin sa ta a mukamin.
Gwamnonin jihohin Najeriya sun yi tir da yadda matsalar man fetur ta ƙi ci ta ƙi cinyewa bayan albarkar mai da ke danƙare a ƙasar, kuma su na ganin haka bai dace ba.
Kungiyar yan kasuwa ta Energies Marketers Association of Nigeria (MEMAN) ta yi martani a kan fargabar za a samu ƙarancin fetur, inda ta karyata lamarin.
Yayin da ƴan Najeriya ke fama da yanayin rayuwa, dillalan mai sun tashi farashin man fetur kwanaki kaɗan bayan NNPCL ya ƙara tsadar lita a gidajen mansa a Najeriya.
Wahalar man fetur a Najeriya
Samu kari